Exodus 23:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kada ku durƙusa wa allolinsu, ko ku yi musu sujada, ko kuma ku bi al’adunsu. Za ku hallaka dukan allolinsu, ku kuma farfasa keɓaɓɓun duwatsunsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَذَاكُ رُسُنَ وَ أَلُّواْلِنْ وَطَنَّنْ أَلْعُمَّيْبَ كُواْ كُيِ مُسُ سُجَّدَ، كُواْ كُبِے أَلْعَادُنْسُ؞ عَمَّا ذَاكُ هَلَّكَرْ دَسُو كَكَڢْ كُكُمَ ڢَرْڢَشٜىٰ دُووَڟُنْ سُجَّدَرْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ba za ku rusuna wa allolinsu ba, balle fa ku bauta musu, kada ku yi yadda suke yi. Sai ku hallaka allolinsu ɗungum, ku farfashe keɓaɓɓun duwatsunsu.