Exodus 23:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Zan aiki razanata a gabanku, in kuma sa ruɗami a cikin kowace al’ummar da za ku sadu da ita. Zan sa duk abokan gābanku su juye da baya, su gudu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كَاڢِنْ كُإِسُواْ وُرِنْ، ذَنْسَا ڟُواْرُواْنَ يَكَامَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ دَ ذَاكُ غَمُ دَسُو، يَسَا سُضِكِثِے؞ ذَنْكُمَسَا دُكَنْ أَبُواْكَنْ غَابَنْكُ سُجُويَا بَايَ سُغُدُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Zan aiki razanata a gabanku, in sa mutanen da za ku gamu da su su ruɗe. Zan sa maƙiyanku duka su ba ku baya, su sheƙa a guje.