Exodus 25:29 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da zinariya zalla kuma za ka yi farantansa, da kwanoninsa na tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin zuban hadayu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ ظِينَارِيَ ظَلَّ ذَاكَيِ ڢَرَنْتَنْسَ دَ تَاسُواْشِنْسَ نَرِڧٜىٰ تُرَارٜىٰ دَ كُمَ بُتُواْثِنْسَ دَ ݣُونُواْنِنْسَ دُواْمِنْ يِنْ هَدَايُ نَأَبِنْ شَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da zinariya tsantsa kuma za ku yi farantansa, da kwanonin tuya, da butocinsa, da kwanoninsa domin yin hadayu na sha.