Exodus 26:1 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ka yi tabanakul da labule goma na lilin mai laushi a naɗe shi biyu, a saƙa labulen da ulu mai ruwan shuɗi, da ulu mai ruwan shunayya, da kuma ulu mai ruwan ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«غَمٜىٰ دَ تٜىٰنْتِنْ كَسَنْثٜىٰوَرْ يَهْوٜىٰهْ كَنْسَ، ذَاكَيِشِ دَ لَبُلٜىٰ غُواْمَ نَظَرٜىٰنْ لِيلِنْ مَيْݣَوْ دَ نَظَرٜىٰنْ سَاڧَ مَيْ كَلَرْ ضُوً بُلَ دَ مَيْ كَلَرْ جَرْ غَرُورَا دَ كُمَ مَيْ كَلَرْ جَ؞ وَطَنَّنْ لَبُلٜىٰ ذَاعَيِ مُسُ أَدُوانْ ذَانِ ذَانِ نَحَلِتُّو مَاسُ ڢِكَڢِكَيْ، عَيْكِنْ ڠُونِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Alfarwar kanta, za ku yi ta da labule goma na lilin mai laushi ninki biyu, da ulu mai launi shuɗi, da launi shunayya da launi ja. Waɗannan labule za a yi musu zānen siffofin kerubobi, aikin gwani.