Exodus 26:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka haɗa labule biyar ka ɗinka. Haka kuma za ka yi da sauran shidan. Ka naɗe shida ɗin biyu, ka yi labulen ƙofar tentin da shi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَهَطَ لَبُلٜىٰ بِيَرْ، كَطِنْكَسُ تَرٜىٰ سُذَمَ لَبُلٜىٰ طَيَ؞ حَكَكُمَ ذَاكَيِ دَ سَوْرَنْ لَبُلٜىٰ شِدَ؞ لَبُلٜىٰ نَشِدَ ذَاكَ نَطٜىٰ شِ بِيُ دُواْمِنْ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ أَغَبَنْ تٜىٰنْتِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ku harhaɗa biyar ku ɗinka. Haka kuma za ku yi da sauran shidan. Ku ninka na shida riɓi biyu, ku yi labulen ƙofar alfarwa da shi.