Exodus 27:11 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A wajen arewa shi ma, tsawon yă zama ƙafa ɗari. Ka kama labulen da ƙugiyoyin da aka yi da azurfa waɗanda aka manna a kan ƙarfen da aka dalaye da azurfa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَكَ مَا ذَاكَيِ وَ إِيَاكَرْ ڢِيلِ تَغٜىٰڢٜىٰنْ أَرٜىٰوَ لَبُلٜىٰ مَاسُ ڟَوُاْ ڧَڢَا طَرِے دَ حَمْسِنْ؞ ذَاعَ رَاتَيَ لَبُلٜىٰنْ أَغِنْشِڧَنْ تَغُلَّ عَشِرِنْ، وَطَنْدَ ذَاعَ تَادَسُو عَكَنْ غِنْدِنْ ذَمَنْسُ غُدَا عَشِرِنْ نَتَغُلَّ؞ ڧُوغِيُواْيِنْ غِنْشِڧَيْ دَ مَطَوْرَنْسُ ذَاعَيِسُ دَ أَظُرْڢَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A wajen arewa kuma, sai ku rataya labule mai tsawon kamu ɗari. Ku yi masa dirkoki da kwasfansu guda ashirin da tagulla, amma ku yi wa dirkokin maratayai da maɗaurai da azurfa.