Exodus 27:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tsayin filin zai zama kamu ɗari, fāɗinsa kuma kamu hamsin, tsayin labulensa na lallausan zaren lilin zai zama kamu biyar, a kuma yi rammukansa da tagulla.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڟَوُانْ إِيَاكَرْ ڢِيلِنْ تٜىٰنْتِنْ غَبَاطَيَ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ ڧَڢَا طَرِے دَ حَمْسِنْ، ڢَاطِنْسَ كُوَ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ ڧَڢَا سَبَعِنْ دَ بِيَرْ، ڟَيِنْسَ كُمَ ڧَڢَا بَݣَويْ دَ رَبِے؞ إِيَاكَرْ ڢِيلِنْ تٜىٰنْتِنْ، ذَاعَ كٜىٰوَيٜىٰشِ دَ لَبُلٜىٰ نَلِيلِنْ مَيْݣَوْ دَ كُمَ غِنْدِنْ ذَمَنْ غِنْشِڧَيْ نَتَغُلَّ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Tsawon farfajiyar zai zama kamu ɗari, fāɗinta kamu hamsin, tsayinta kamu biyar. Za a saƙa labulenta da lallausan zaren lilin, a kuma yi kwasfanta da tagulla.