Exodus 27:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A cikin Tentin Sujada, a waje da labulen da yake a gaban Akwatin Alkawari, Haruna da ’ya’yansa za su sa fitilu su yi ta ci a gaban Ubangiji, daga yamma har safiya. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a cikin Isra’ila har tsararraki masu zuwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاعَ أَجِيٜىٰ سَنْدَا مَيْ رِڧٜىٰ ڢِتِلُ أَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے، أَغَبَنْ لَبُلٜىٰنْ دَيَكٜىٰ رُڢٜىٰ عَݣُوتِنْ شَيْدَرْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَرْ دَيَكٜىٰ ثِكِنْ وُرِے مَڢِے ڟَرْكِے؞ هَٰرُونَ دَ یَیَنْسَ مَظَا ذَاسُ كُلَ دَ ڢِتِلُ دَرٜىٰ دَ رَانَ دُواْمِنْ سُيِتَثِ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ وَنَّنْ ڧَٰعِدَ ثٜىٰ تَدِنْدِنْدِنْ دُواْمِنْ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكِيَايٜىٰ دَغَ نَنْ حَرْ ذُوَا إِيَاكَرْ ڟَارَرْسُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za a ajiye ta a cikin alfarwar a gaban labule na wurin shaida. Haruna da 'ya'yansa za su lura da ita daga safiya har maraice. Wannan zai zama ka'ida har abada ga Isra'ilawa.”