Exodus 27:3 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka yi duk kayan aikinsa da tagulla, tukwanensa na ɗiban toka, da manyan cokula, da kwanonin yayyafawa, da cokula masu yatsotsi don nama da kuma farantai domin wuta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكَيِ تُݣُونٜىٰنْ ڧَرْڢٜىٰ دُواْمِنْ عَتَارَ تُواْكَرْ بَغَدٜىٰ دَ كُمَ شٜىٰبُرُواْرِ دَ مَنْيَنْ ݣُونُواْنِ دَ ثُواْكُلَ مَاسُ يَڟُ دَ كُمَ ݣُونُواْنِ نَݣُوشِ غَرْوَشِنْ وُتَا؞ دُكَنْ وَطَنَّنْ كَايَنْ عَيْكِ، ذَاعَيِ سُونٜىٰ دَ تَغُلَّ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za ku ƙera kwanoni domin tokar bagade, da manyan cokula da daruna, da cokula masu yatsotsi, da kuma farantai domin wuta. Za ku ƙera dukan kayayyakin bagaden da tagulla.