Exodus 28:15 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ka shirya ƙyallen da za a manna a ƙirji don neman nufin Allah. Sai a saƙa shi da gwaninta kamar yadda aka saƙa efod ɗin. A saƙa shi da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«ذَاكَيِ أَلْجِهُنْ ڧِرْجِ نَ عٜىٰڢُوادْ، وَتُواْ عٜىٰڢُوادْ نَنٜىٰمَنْ سَنِنْ نُڢِنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ ذَاعَيِشِ دَ ظَرٜىٰ إِرِنَّ عٜىٰڢُوادْ، وَتُواْ ظَرٜىٰنْ سَاڧَ نَظِينَارِيَ دَ نَمَيْ كَلَرْ ضُوً بُلَ دَ مَيْ كَلَرْ جَرْ غَرُورَا دَ مَيْ كَلَرْ جَا دَ ظَرٜىٰنْ لِيلِنْ مَيْݣَوْ، عَيْكِنْ ڠُونِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Ku kuma yi ƙyallen maƙalawa a ƙirji domin neman nufin Allah. Sai a saƙa shi da gwaninta kamar yadda aka saƙa falmaran ɗin. A saƙa shi da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan zaren lilin.