Exodus 28:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka ƙara zobai biyu, ka kuma ɗaura su a bakin ƙyallen da ya sauka daga kafaɗa ta gaban efod, kusa da mahaɗin ƙyallaye biyu a bisa ɗamara na efod.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكَ ڧَارَ يِنْ وَطَنْسُ ذُواْبٜىٰ بِيُ نَظِينَارِيَ، كَسَا طَيَ عَكَنْ كُواْوَنٜىٰ أَبِنْ رَاتَيَ أَلْجِهُنْ عَتَغَبَ دَيْدَيْ عِنْدَ مَهَطِنْ طَمَرَ مَيْ أَدُواْ يَكٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ku kuma yi waɗansu ƙawanya biyu na zinariya, a sa su a ƙashiyar kafaɗu biyu na falmaran daga gaba, a sama da abin ɗamaran nan.