Exodus 28:38 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai kasance a goshin Haruna, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra’ilawa sun yi cikin miƙa baye-bayensu masu tsarki. Zai kasance a goshin Haruna kullayaumin, domin su zama abin karɓa ga Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
تَهَكَ إِنْ هَٰرُونَ يَسَا هُولَرْ ڢِرِسْتِ، رُبُوتُنْ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ أَغُواْشِنْسَ؞ تَهَكَ كُمَ هَٰرُونَ ذَيْ طَوْكِ نَوْيِنْ كُسْكُرُواْرِنْ دَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُنْيِ لُواْكَثِنْ دَ سُكَ مِيڧَ بَيٜىٰ بَيٜىٰنْسُ مَاسُ ڟَرْكِے؞ كُلُّمْ رُبُوتُنْ ذَيْ كَسَنْثٜىٰ أَغُواْشِنْ هَٰرُونَ دُواْمِنْ بَيٜىٰ بَيٜىٰنْ سُذَمَ أَبِنْ كَرْٻَ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haruna kuwa zai sa shi bisa goshinsa, ta haka zai ɗauki kurakuran da ya yiwu Isra'ilawa sun yi cikin miƙa sadakokinsu masu tsarki. Kullum Haruna zai riƙa sa shi bisa goshinsa don su zama karɓaɓɓu ga Ubangiji.