Exodus 28:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗannan su ne tufafin da za su ɗinka, ƙyallen maƙalawa a ƙirji, da efod, da taguwa, da doguwar riga, da rawani, da abin ɗamara. Za su yi wa ɗan’uwanka, Haruna da ’ya’yansa, waɗannan tsarkaka tufafi, don su zama firistoci masu yi mini hidima.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا رِيغُنَنْ دَ ذَاسُ طِنْكَ، أَلْجِهُنْ ڧِرْجِ نَ عٜىٰڢُوادْ دَ عٜىٰڢُوادْ دَ دُواْغُوَرْ رِغَا دَ غَجٜىٰرِيَرْ رِغَا مَيْ أَدُوانْ سَاڧَ نَهَنُّ دَ هُولَرْ ڢِرِسْتِ دَ أَبِنْ طَمَرَ؞ ذَاسُ طِنْكَ رِيغُنَنَّنْ نَنُونَ كٜىٰٻٜىٰوَرْ طَنْعُوَنْكَ هَٰرُونَ دَ یَیَنْسَ، دُواْمِنْ سُيِ مِنِ حِدِمَرْ ڢِرِسْتِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Waɗannan su ne irin tufafin da za su ɗinka, ƙyallen maƙalawa a ƙirji, da falmaran, da taguwa, da zilaika, da rawani, da abin ɗamara. Za su yi wa ɗan'uwanka, Haruna, da 'ya'yansa tufafi tsarkaka, don su zama firistoci masu yi mini aiki.