Exodus 28:43 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Dole Haruna da ’ya’yansa su sa su sa’ad da za su shiga Tentin Sujada, ko sa’ad da suka kusace bagade domin hidima a Wuri Mai Tsarki, don kada su yi laifi, su kuma mutu. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla wa Haruna da zuriyarsa har abada.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُواْلٜىٰ هَٰرُونَ دَ یَیَنْسَ مَظَا سُسَا سَعَدَّ سُكٜىٰ شِغَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے، كُواْ كُوَ سَعَدَّ سُكَيِ كُسَدَ بَغَدٜىٰ عَثِكِنْ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے دُواْمِنْ يِنْ حِدِمَرْسُ، دُواْمِنْ كَدَ سُيِ لَيْڢِنْدَ ذَيْ جَٰوُاْ مُسُ مُتُوَ؞ وَنَّنْ يَذَمَ ڧَٰعِدَثٜىٰ تَدِنْدِنْدِنْ غَ هَٰرُونَ دَ ذُرِيَرْسَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haruna da 'ya'yansa maza za su sa su sa'ad da suke shiga alfarwa ta sujada ko kuwa sa'ad da suka kusaci bagade domin su yi aiki cikin Wuri Mai Tsarki domin kada su yi laifin da zai zama sanadin mutuwarsu. Wannan zai zama doka ga Haruna da zuriyarsa har abada.”