Exodus 29:20 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka yanka ragon, ka ɗibi jinin, ka shafa a bisa leɓen kunnen Haruna na dama, da bisa leɓen kunnuwan ’ya’yansa maza na dama, da kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi kewaye da gefen bagaden.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً كَايَنْكَ ضَغُوانْ كَتَرٜىٰ جِنِنْ؞ كَطِبِے جِنِنْ ضَغُوانْ كَسَا أَ لٜىٰٻٜىٰنْ كُنّٜىٰنْ دَامَ نَ هَٰرُونَ دَ نَیَیَنْسَ مَظَا؞ كَكُمَسَا عَكَنْ مَنْيَنْ يَڟُ نَهَنُّوَنْسُ نَدَمَ دَ نَڧَڢَاڢُنْسُ نَدَمَ؞ سَعَنً كَيَيَّڢَا سَوْرَ جِنِنْ عَكُواْوَنٜىٰ غٜىٰڢٜىٰنْ بَغَدٜىٰنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan ka yanka ragon, ka ɗibi jininsa ka shafa bisa leɓatun kunnen Haruna na dama, da bisa leɓatun kunnuwan 'ya'yansa maza na dama, da a kan manyan yatsotsin hannuwansu na dama, da kuma a kan manyan yatsotsin ƙafafunsu na dama. Sauran jinin kuwa, sai ka yayyafa shi a kewaye a kan bagaden.