Exodus 29:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ka ɗebi kitse daga wannan rago, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebi kitsen da ya rufe kayan ciki, da kitsen da yake bisa hanta, da ƙoda biyu da kitsen da yake kansu, da cinyar dama. (Gama rago ne don naɗi.)
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«ذَاكَ ثِرٜىٰ كِڟٜىٰنْ ضَغُوانْ دَ كِڟٜىٰنْ وُڟِيَرْ دَ كِڟٜىٰنْدَ يَرُڢٜىٰ كَايَنْ ثِكِ دَ سَاشٜىٰ مَڢِے ݣَوْ نَهَنْتَ دَ ڧُواْدَ بِيُ دَ كِڟٜىٰنْدَ يَرُڢٜىٰسُ دَ ثِنْيَرْ دَامَ، تُنْدَيَكٜىٰ وَنَّنْ ضَغُواْ نَنَطَوَرْ ڢِرِسْتِنٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Sai ka ɗebe kitsen ragon, ka yanke wutsiyarsa mai kitse, ka kuma ɗebe kitsen da yake rufe da kayan ciki, da dunƙulen kitsen da yake a bisa hanta, da ƙoda biyu ɗin da kitsensu, da cinyar dama, gama ragon na keɓewa ne.