Exodus 29:26 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Bayan haka, ka ɗauki ƙirjin ragon domin naɗin Haruna, ka kaɗa shi a gaban Ubangiji kamar hadaya ta kaɗawa. Wannan ƙirji zai zama rabonka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«ذَاكَ طَوْكِ ڧِرْجِنْ ضَغُوانْ دَ عَكَ يَنْكَ دُواْمِنْ نَطَوَرْ هَٰرُونَ، كَطَغَشِ سَمَ يَذَمَ هَدَايَ تَطَغَوَ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ ؞ وَنَّنْ ڧِرْجِنْ ذَيْ ذَمَ رَبُوانْكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Za ka ɗauki ƙirjin ragon da aka yanka don keɓewar Haruna, ka kaɗa shi don hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Wannan ƙirji zai zama rabonka.