Exodus 29:40 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Haɗe da ɗan rago na farkon, ka miƙa mudun gari mai laushi wanda an gauraye da kwalaba ɗaya na tataccen mai zaitun, da kwalaba ɗaya na ruwan inabi don hadaya ta sha.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَطٜىٰ دَ طَنْ ضَغُواْ نَڢَرْكُوانْ، ذَاعَ مِيڧَ كِلُواْ طَيَ نَغَارِنْ أَلْكَمَ مَيْ لَوْشِ وَنْدَ عَكَ ݣُوٻَ دَ لِتَ طَيَ نَمَنْ ظَيْتُنْ دَ عَكَ تَاثٜىٰ؞ كُمَ ذَاعَ ظُبَ لِتَ طَيَ نَضُوً إِنَبِے دُواْمِنْ هَدَايَ تَأَبِنْ شَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haɗe da rago na fari, za a miƙa mudun gari mai laushi garwaye da rubu'in moɗa na tataccen mai, da rubu'in moɗa na ruwan inabi domin hadaya ta sha.