Exodus 29:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka ɗauki rigar ka sa wa Haruna, ka sa masa doguwar rigar, da rigar efod, da efod kanta, da ƙyallen maƙalawa a ƙirji. Ka ɗaura masa efod da ɗamarar da aka yi mata ado.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً كَطَوْكِ رِيغُنَنْ كَسَاوَ هَٰرُونَ؞ كَڢَارَ دَ دُواْغُوَرْ رِغَرْ، كَبِدَ غَجٜىٰرِيَرْ رِغَرْ، كَسَا رِغَرْ عٜىٰڢُوادْ، كَسَا أَلْجِهُنْ ڧِرْجِ نَ عٜىٰڢُوادْ عَكَيْ، سَعَنً كَطَوْرَ مَسَ أَبِنْ طَمَرَ وَنْدَ عَكَيِ مَسَ أَدُوانْ سَاڧَ نَهَنُّ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan ka kawo tufafin, ka sa wa Haruna zilaikar, da taguwar falmaran, da falmaran ɗin, da ƙyallen maƙalawa a ƙirji, sa'an nan ka ɗaura masa ɗamarar falmaran wadda aka yi mata saƙar gwaninta.