Exodus 3:18 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Dattawan Isra’ila za su saurare ka. Sa’an nan da kai da dattawan Isra’ila, za ku tafi wurin sarkin Masar, ku ce masa, ‘ Ubangiji, Allah na Ibraniyawa, ya sadu da mu. Bari mu yi tafiyar kwana uku zuwa cikin hamada domin mu yi hadaya wa Ubangiji Allahnmu.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
« ‹مُتَنٜىٰنْ كُوَ ذَاسُ كَسَ كُنّٜىٰ غَ مَغَنَرْكَ؞ سَعَنً كَيْ دَ دَتَّاوَنْ جَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ ذَاكُتَڢِے وُرِنْ سَرْكِنْ مَصَرْ كُثٜىٰ مَسَ « يَهْوٜىٰهْ ، اللَّهْ نَ إِبْرَانِيَاوَا يَا بَيَّنَ أَغَرٜىٰمُ؞ يَنْذُ ڢَا، سَيْ كَبَرْمُ مُيِ تَڢِيَرْ ݣُونَ عُكُ ذُوَا ثِكِنْ دَاجِ، دُواْمِنْ مُمِيڧَ هَدَايَ غَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْمُ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za su kasa kunne ga muryarka. Sa'an nan kai da dattawan Isra'ila za ku tafi gaban Sarkin Masar ku ce masa, ‘Ubangiji Allah na Ibraniyawa ya gamu da mu. Yanzu fa, muna roƙonka, ka yarda mana mu yi tafiyar kwana uku a cikin jeji mu miƙa masa hadaya.’