Exodus 3:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kowace mace ta tambayi maƙwabciyarta, da kuma duk wata macen da take cikin gidanta, kayayyakin azurfa da na zinariya da kuma na riguna, waɗanda za ku sa wa ’ya’yanku maza da mata. Ta haka nan za ku washe Masarawa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْوَثٜىٰ مَثٜىٰ ذَاتَ تَڢِے تَضُواْڧِ كَايَنْ دَرَجَ نَأَظُرْڢَا دَ نَظِنَرِيَ دَ رِيغُنَ دَغَ وُرِنْ مَتَنْ مَصَرْ دَسُكٜىٰ مَڨُوبْتَنْتَ دَ وَطَنْدَ سُكٜىٰ ذَمَ أَغِدَاجٜىٰنْسُ؞ ذَاكُسَا وَیَیَنْكُ مَظَا دَ مَاتَا وَطَنَّنْ كَايَيَّكِ؞ تَهَكَ ذَاكُ ݣُوشِ أَرْزِڧِنْ مَصَرَاوَا؞› »
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma kowace mace za ta roƙi maƙwabciyarta da wadda take cikin gidanta kayan ado na azurfa, da na zinariya, da tufafi, za ku sa wa 'ya'yanku mata da maza. Da haka za ku washe Masarawa.”