Exodus 3:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Allah ya ce, “Ni ne Allah na kakanninka, Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub.” Da jin wannan, sai Musa ya ɓoye fuskarsa, domin ya ji tsoro yă dubi Allah.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
نِنٜىٰ اللَّهْ نَكَاكَنِّنْكَ، وَتُواْ اللَّهْ نَ إِبْرَٰهِيمْ، اللَّهْ نَ إِسْحَٰڧَ، اللَّهْ نَ يَعْڧُوبَ؞» سَعَدَّ مُوسَٰى يَا جِ وَنَّنْ، يَرُڢٜىٰ ڢُسْكَرْسَ غَمَا يَنَ جِنْ ڟُواْرُواْ يَدُوبِے اللَّهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya kuma ce, “Ni ne Allah na kakanninka, wato Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.” Sai Musa ya ɓoye fuskarsa, gama yana jin tsoro ya dubi Allah.