Exodus 30:12 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Sa’ad da za ku ƙidaya Isra’ilawa, dole kowanne yă biya domin yă fanshe kansa ga Ubangiji a lokacin da aka ƙidaya shi. Ta haka babu wata annobar da za tă buge su sa’ad da kuke ƙidaya su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«سَعَدَّ ذَاكَ ڧِرْغَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، أَ لُواْكَثِنْ، كُواْوَنٜىٰ مُتُمْ ذَيْبِيَ هَرَاجِ غَ يَهْوٜىٰهْ دُواْمِنْ يَڢَنْشِ رَنْسَ، دُواْمِنْ كَدَ بَلَعِ يَڢَاطُواْ عَثِكِنْ مُتَنٜىٰنْ يَايِنْ دَ عَكٜىٰ لِسَّڢْتَاسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“A sa'ad da za ku ƙidaya Isra'ilawa, sai ko wannensu ya biya fansar kansa ga Ubangiji domin kada annoba ta buge su lokacin da za ku ƙidaya su.