Exodus 30:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kowannen da ya ƙetare zuwa wurin waɗanda aka riga aka ƙidaya, dole yă ba da rabin shekel, bisa ga ma’aunin shekel na tsattsarkan wuri, wanda nauyinsa garwa ashirin ne. Wannan rabin shekel hadaya ce ga Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا أَبِنْدَ دُكْ وَنْدَ عَكَ ڧِرْغَ ذَيْبِيَ، رَبِنْ مَعَوْنِنْ أَظُرْڢَا بِسَغَ مَعَوْنِنْ دَ عَكٜىٰ أَمْڢَانِ دَشِ أَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے؞ كُواْوَنٜىٰ مُتُمْ ذَيْبِيَ وَنَّنْ، بَيْكُواْ غَ يَهْوٜىٰهْ كٜىٰنَنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan wanda aka lasafta shi cikin ƙidayar kuwa zai biya kuɗi bisa ga ma'aunin kuɗin da ake aiki da shi. Tilas kowanne ya biya wannan, gama sadaka ce ga Ubangiji.