Exodus 30:36 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ka ɗiba kaɗan daga ciki, ka niƙa, ka ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin Tentin Sujada, inda zan sadu da kai. Zai zama mafi tsarki a gare ku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكَ طِبَ كَطَنْ دَغَ ثِكِ كَدَكَشِ يَذَمَ غَارِ، كَيَيَّڢَا شِ أَغَبَنْ عَݣُوتِنْ شَيْدَرْ يَرْجٜىٰجٜىٰنِيَ عَثِكِنْ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ عِنْدَ ذَنْسَدُ دَكَيْ؞ وَنَّنْ تُرَارٜىٰ ذَيْ ذَمَ مُكُ أَبُ مَيْ ڟَرْكِے سُواْسَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ɗauki kaɗan daga ciki, a niƙa, sa'an nan a ɗiba daga ciki, a ajiye a gaban akwatin alkawari a cikin alfarwa ta sujada a inda zan sadu da kai. Wannan turare zai zama muku mafi tsarki.