Exodus 31:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Ka faɗa wa Isra’ilawa, ‘Dole ku kiyaye Asabbataina. Wannan zai zama alama tsakanina da ku daga tsara zuwa tsara, saboda ku sani ni ne Ubangiji, wanda ya mai da ku masu tsarki.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كَيْ كَڢَطَا وَمُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ، ‹لَلَّيْ نٜىٰ كُكِيَايٜىٰ رَانَكُنْ دَيْنَ عَيْكِ وَطَنْدَ نَبَاكُ، غَمَا وَنَّنْ عَلَمَ ثٜىٰ ڟَكَانِينَ دَكُو دَغَ نَنْ حَرْ إِيَاكَرْ ڟَارَرَّكِنْكُ، دُواْمِنْ كُسَنِ ثٜىٰوَ نِے يَهْوٜىٰهْ نٜىٰ نَكٜىٰٻٜىٰكُ دَ ڟَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Faɗa wa Isra'ilawa, ‘Sai ku kiyaye Asabar domin shaida tsakanina da ku da zuriyarku har abada, domin ku sani ni ne Ubangiji wanda ya keɓe ku.