Exodus 31:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ ‘Ku kiyaye Asabbaci, domin yă zama mai tsarki a gare ku. Duk wanda ya ƙazantar da shi, za a kashe shi; duk wanda ya yi wani aiki a ranar, za a ware shi daga mutane.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ذَاكُ ڢَا كِيَايٜىٰ رَانَرْ هُوتُ تَمَكُواْ، غَمَا رَانَ ثٜىٰ مَيْ ڟَرْكِے أَغَرٜىٰكُ؞ دُكْ وَنْدَ يَيِ بَنْظَ دَ عِتَ ذَاعَ كَشٜىٰشِ، دُكْ وَنْدَ يَيِ عَيْكِ عَثِكِنْتَ، ذَاعَ كَوَرْ دَشِ دَغَ ثِكِنْ جَمَعَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ku kiyaye ranar Asabar gama tsattsarkar rana ce a gare ku. Duk wanda ya tozarta ta, za a kashe shi, duk wanda ya yi aiki kuma a cikinta za a raba shi da jama'arsa.