Exodus 32:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai na gaya musu, ‘Duk wanda yana da kayan ado na zinariya, ya cire?’ Sa’an nan suka ba ni zinariya, sai na jefa cikin wuta, wannan ɗan maraƙi ya fito.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
شِيَسَا نَثٜىٰ مُسُ، ‹دُكْ وَنْدَ يَكٜىٰدَ ظِينَارِيَ، سَيْ يَكَٰوُاْ مِنِ سُو!› سَعَدَّ سُكَ كَٰوُاْ مِنِ، نَظُبَرْ دَسُو عَثِكِنْ وُتَا، سَيْغَا وَنَّنْ صِڢَّرْ طَنْ بِجِمِ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ni kuwa sai na ce musu, ‘Bari duk wanda yake da zinariya ya tuɓe.’ Waɗanda suke da ita, suka tuɓe, suka kawo mini, ni kuwa na zuba su cikin wuta, daga nan wannan maraƙi ya fito.”