Exodus 32:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sun yi saurin juyawa daga abin da na umarce su, sun kuma yi wa kansu gunki na siffar ɗan maraƙi. Sun yi sujada ga ɗan maraƙi, suka yi hadaya gare shi, suka kuma ce, waɗannan su ne allolinka ya Isra’ila, waɗanda suka fito da kai daga Masar.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُنْيِ سَوْرِنْ كَوْثٜىٰوَ دَغَ حَنْيَرْدَ نَعُمَرْثٜىٰسُ سُبِے؞ سُنْ ڧٜىٰرَ وَكَنْسُ صِڢَّرْ طَنْ بِجِمِ سُنَيِ مَسَ سُجَّدَ، حَرْ سُنَ مِيڧَ مَسَ هَدَايَ سُنَ ثٜىٰوَ ‹يَا إِسْرَٰٓءِيلَ، وَنَّنْ شِينٜىٰ اللَّهْ وَنْدَ يَڢِتَرْ دَكُو دَغَ ڧَسَرْ مَصَرْ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sun yi saurin kaucewa daga hanyar da na umarce su. Sun yi wa kansu ɗan maraƙi na zubi, sun yi masa sujada, sun miƙa masa hadaya, sun kuma ce, ‘Ya Isra'ila, wannan shi ne allahn da ya fisshe ka daga ƙasar Masar.”’