Exodus 33:7 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Musa fa ya saba ɗaukan tenti yă kafa shi a bayan sansani da ɗan nisa, yana kiransa “Tentin Sujada.” Duk wanda yake neman wani abu daga wurin Ubangiji sai yă tafi Tentin Sujada a bayan sansani.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُوسَٰى كُوَ يَكَنْ طَوْكِ تٜىٰنْتِنْ دَيَكٜىٰ كِرَا دَ سُونَنْ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ يَكَڢَ شِ عَبَايَنْ ذَنْ‌غُوانْ؞ دُكْ وَنْدَ يَكٜىٰ نٜىٰمَنْ سَنِنْ نُڢِنْ يَهْوٜىٰهْ ذَيْ تَڢِے وُرِنْ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ، وَنْدَ يَكٜىٰ عَبَايَنْ ذَنْ‌غُوانْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Musa ya ɗauki alfarwa, ya kafa ta a bayan zango, nesa da zango. Ya kuwa sa mata suna, Alfarwa ta Sujada. Duk wanda yake neman Ubangiji, sai ya tafi alfarwa ta sujada, wanda yake a bayan zango.