Exodus 34:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku fanshi ɗan farin jaki da na tunkiya, amma in ba ku fanshe shi ba, ku karya wuyansa. Ku fanshi duk ’ya’yan farinku maza. “Kada wani yă zo gabana hannu wofi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا ذَاكَ ڢَنْشِ كُواْوَنٜىٰ طَنْ ڢَارِ نَجَاكُنَ دَغَ وُرِنْ يَهْوٜىٰهْ تَوُرِنْ بَادَ طَنْ ضَغُواْ أَمَدَدِنْسَ؞ عَمَّا عِدَنْ بَذَاكَ ڢَنْشٜىٰشِ بَ، سَيْ كَكَرْيَ وُيَنْسَ؞ كُواْوَنٜىٰ طَنْ ڢَضٍ یَیَنْكَ، ذَاكَ ڢَنْشٜىٰشِ؞ «كَدَ وَنِ يَذُواْ غَبَنَ حَنُّ وُاْڢِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ɗan farin jaki kuwa za ku fansa da ɗan rago, in kuwa ba za ku fansa da ɗan rago ba, sai ku karya wuyansa. Za ku fanshi kowane ɗan fari. Kada a sami wanda ya zo gabana hannu wofi.