Exodus 35:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
duk waɗanda suke da niyya, waɗanda kuma zukatansu suka motsa su, suka kawo kyautai wa Ubangiji, don aikin Tentin Sujada, don duk aikinsa, da don tsarkakakkun riguna.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَ دَاوُاْ؞ دُكْ وَنْدَ ذُوثِيَارْسَ تَتَٻَشِ دَ وَنْدَ رُوحُنْسَ يَمُواْڟَشِ يَكَٰوُاْ وَ يَهْوٜىٰهْ بَيْكُوانْسَ دُواْمِنْ عَيْكِنْ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ دَ دُكَنْ كَايَيَّكِ نَحِدِمَرْسَ دَ رِيغُنَنْسَ مَاسُ ڟَرْكِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk wanda ya yi niyya, da wanda ruhunsa ya iza shi ya kawo wa Ubangiji sadaka don yin alfarwa ta sujada, da dukan ayyukansa, da tsarkakakkun tufafi.