Exodus 35:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kowane mutumin da yake da shuɗi, shunayya ko jan zare, ko lallausan lilin, ko gashin akuya, ko fatun rago da aka rina ja, ko fatun shanun teku, suka kawo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ وَنْدَ يَكٜىٰدَ ظَرٜىٰنْ سَاڧَ مَيْ كَلَرْ ضُوً بُلَ، كُواْ مَيْ كَلَرْ جَرْ غَرُورَا، كُواْ مَيْ كَلَرْ جَ، كُواْ ظَرٜىٰنْ لِيلِنْ مَيْݣَوْ، كُواْ ظَرٜىٰنْ غَاشِنْ عَكُيَ، كُواْ ڢَتُنْ رَغُنَ وَطَنْدَ عَكَ ڠَرَ، كُواْ ڢَتُ مَاسُ ݣَوْ سُكَ كَٰوُاْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kowane mutum da aka iske shi yana da shuɗi, ko shunayya, ko mulufi, ko lallausan lilin, ko gashin awaki, ko fatun raguna da aka rina suka zama ja, ko fatun awaki, ya kawo su.