Exodus 35:24 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Masu miƙa kyautar azurfa, ko tagulla suka kawo su a matsayin kyautai ga Ubangiji, kuma kowane mutumin da yake da itacen ƙirya don kowane sashin aikin, ya kawo.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْ وَنْدَ يَ عِيَ كَٰوُاْ بَيْكُواْ نَأَظُرْڢَا، كُواْ نَتَغُلَّ يَكَٰوُاْشِ بَيْكُواْ غَ يَهْوٜىٰهْ ؞ دُكْ وَنْدَ يَكٜىٰدَ إِتَاثٜىٰنْ عَكَشِيَ وَنْدَ يَكٜىٰدَ أَمْڢَانِ وُرِنْ عَيْكِنْ، شِے مَا يَكَٰوُاْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kowane ne wanda ya iya, ya ba da sadaka ta azurfa, da ta tagulla ga Ubangiji. Duka kuma wanda aka iske shi yana da itacen ƙirya wanda zai yi amfani a cikin aikin, ya kawo shi.