Exodus 35:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kowace mace mai fasaha ta kaɗa zare da hannuwanta, ta kuma kawo abin da ta kaɗa na shuɗi, shunayya, ko jan zare, ko lallausan lilin.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ مَتَ مَاسُ عِيَيِنْ ظَرٜىٰ، سُكَيِ سُكَ كَٰوُاْ ظَرٜىٰ مَيْ كَلَرْ ضُوً بُلَ دَ مَيْ كَلَرْ جَرْ غَرُورَا دَ مَيْ كَلَرْ جَا دَ ظَرٜىٰنْ لِيلِنْ مَيْݣَوْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Dukan mata masu hikima suka kaɗa zare da hannuwansu, suka kawo zaren da suka kaɗa na shuɗi, da shunayya, da mulufi, da lallausan lilin.