Exodus 37:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka yi wurin ajiye fitila da zinariya zalla, suka yi gindinsa da kuma gorar jikinsa, da ƙerarriyar zinariya. Kwaf wurin ajiye fitila da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da wurin ajiye fitilan.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ ظِينَارِيَ ظَلَّ يَيِ سَنْدَا مَيْ رِڧٜىٰ ڢِتِلُ؞ سَنْدَنْ دَ غِنْدِنْ ذَمَنْسَ دَ ݣُوڢُنَنْسَ وَطَنْدَ يَيِسُ ثِكِنْ صِڢَّرْ ڢُلَوَرْ أَلْمُوانْ تَرٜىٰدَ كُنّٜىٰنْ ڢُلَوَرْسَ دَ تُواْهُوانْسَ، يَڧٜىٰرَسُ أَ حَطٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya yi alkuki da zinariya tsantsa. An yi gindinsa da gorar jikinsa da ƙerarriyar zinariya. Ƙoƙunan alkukin da mahaɗansa, da furanninsa, a haɗe aka yi su da alkukin.