Exodus 38:11 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Tsawon labule na wajen gefen arewa kamu ɗari ne, yana kuma da sanduna guda ashirin da rammuka ashirin na tagulla, da ƙugiyoyin azurfa da maɗaurai a kan sandunan.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
حَكَ مَا عَكَيِ وَ إِيَاكَرْ ڢِيلِ تَغٜىٰڢٜىٰنْ أَرٜىٰوَ لَبُلٜىٰ مَاسُ ڟَوُاْ ڧَڢَا طَرِے دَ حَمْسِنْ؞ عَكَ رَاتَيَ لَبُلٜىٰنْ أَغِنْشِڧَنْ تَغُلَّ عَشِرِنْ، وَطَنْدَ عَكَ تَادَسُو عَكَنْ غِنْدِنْ ذَمَنْسُ غُدَا عَشِرِنْ نَتَغُلَّ؞ ڧُوغِيُواْيِنْ غِنْشِڧَيْ دَ مَطَوْرَنْسُ، عَكَيِسُ دَ أَظُرْڢَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Tsawon labule na wajen gefen arewa kamu ɗari ne. An yi dirkokinsa guda ashirin da kwasfansu ashirin da tagulla, amma an yi maratayan dirkoki da maɗaurai da azurfa.