Exodus 38:26 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk mutumin da ya shiga ƙirge daga mai shekaru ashirin zuwa gaba, ya ba da rabin shekel. Mazan da suka shiga ƙirge sun kai mutum 603,550.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْوَنٜىٰ مُتُمِنْ دَ عَكَ لِسَّڢْتَا، وَطَنْدَ شٜىٰكَرُنْسُ سُكَ كَيْ عَشِرِنْ ذُوَا سَمَ، يَبَادَ رَبِنْ مَعَوْنِنْ أَظُرْڢَا بِسَغَ مَعَوْنِنْ دَ عَكٜىٰيِنْ أَمْڢَانِ دَشِ أَ وُرِے مَيْ ڟَرْكِے؞ وَطَنَّنْ مُتَنٜىٰ سُنْ كَيْ مُتُمْ دُبُو طَرِے شِدَ دَ دُبُو عُكُ دَ طَرِے بِيَرْ دَ حَمْسِنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kowane mutum da aka ƙidaya ya ba da rabin shekel. Duk mai shekara ashirin ko fi an ƙidaya shi, aka sami maza dubu ɗari shida da dubu uku da ɗari biyar da hamsin (603,550).