Exodus 39:20 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan suka yi waɗansu ƙarin zobai biyu na zinariya, suka maƙale su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na efod kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar efod.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَ ڧَارَيِنْ وَطَنْسُ ذُواْبٜىٰ بِيُ نَظِينَارِيَ، عَكَسَا طَيَ عَكَنْ كُواْوَنٜىٰ أَبِنْ رَاتَيَ أَلْجِهُنْ عَتَغَبَ دَيْدَيْ عِنْدَ مَهَطِنْ طَمَرَ مَيْ أَدُواْ يَكٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka yi waɗansu ƙawane biyu na zinariya, suka maƙala su daga ƙasa a gaban kafaɗu biyu na falmaran kusa da mahaɗin a bisa abin ɗamarar falmaran.