Exodus 39:5 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gwanin mai saƙa ya saƙa abin ɗamarar efod. Da irin kayan da aka saƙa efod ne aka saƙa abin ɗamarar, wato, da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da jan zare, da zaren lallausan lilin, yadda Ubangiji ya umarci Musa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَبِنْ طَمَرَ مَيْ أَدُوانْ ڠُونِنْ طِنْكِ، عَكَيِشِ دَ إِرِنْ طِنْكِ نَ عٜىٰڢُوادْ دَ ظَرٜىٰنْ سَاڧَ إِرِنْ نَ عٜىٰڢُوادْ، وَتُواْ ظَرٜىٰنْ سَاڧَ نَظِينَارِيَ دَ نَمَيْ كَلَرْ ضُوً بُلَ دَ مَيْ كَلَرْ جَرْ غَرُورَا دَ مَيْ كَلَرْ جَا دَ كُمَ ظَرٜىٰنْ لِيلِنْ مَيْݣَوْ، بِسَغَ يَدَّ يَهْوٜىٰهْ يَعُمَرْثِ مُوسَٰى؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gwanin masaƙi ya saƙa abin ɗamarar falmaran. Da irin kayan da aka saƙa falmaran ne aka saƙa abin ɗamarar, wato da zinariya, da shuɗi, da shunayya, da mulufi, da zaren lallausan lilin kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.