Exodus 5:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Manyan Isra’ilawa waɗanda shugabannin gandun Fir’auna suka naɗa, suka sha dūka, aka kuma yi musu tambayoyi ana cewa, “Don me ba ku cika yawan tubula na jiya da na yau kamar yadda kuka saba ba?”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَكَ بُلَلِ إِسْرَٰٓءِيلَاوَا مَاسُ لُورَ دَ عَيْكِ، وَطَنْدَ شُوغَبَنِّنْ عَيْكِنْ دُواْلٜىٰ سُكَسَا عَبِسَنْسُ، سُكَثٜىٰ مُسُ «مٜىٰيَسَا جِيَ دَ يَوْ بَكُ ثِكَ يَوَنْ بُلُواكْ دَ دَا كُكَنْيِبَ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Aka kuwa bulali manya waɗanda suke Isra'ilawa waɗanda shugabannin aikin gandu na Fir'auna suka sa a bisa Isra'ilawa, ana cewa, “Me ya sa jiya da yau ba ku cika yawan tubalin da aka ƙayyade, kamar dā ba?”