Exodus 5:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai suka ce, “Allah na Ibraniyawa ya sadu da mu. Yanzu bari mu ɗauki tafiyar kwana uku cikin hamada domin mu miƙa hadaya ga Ubangiji Allahnmu, don kada yă buga mu da annoba ko takobi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُوسَٰى دَ هَٰرُونَ سُكَ أَمْسَ سُكَثٜىٰ «اللَّهْ نَ إِبْرَانِيَاوَا يَا بَيَّنَ كَنْسَ أَغَرٜىٰمُ؞ مُنَ ضُواْڧُوانْكَ كَبَرْمُ مُيِ تَڢِيَ تَݣُونَ عُكُ ذُوَا ثِكِنْ دَاجِ دُواْمِنْ مُمِيڧَ هَدَايُ غَ يَهْوٜىٰهْ اللَّهْ نْمُ؞ غَمَا إِنْ بَمُ تَڢِے بَ، ذَيْ هَلَكَامُ دَ بَلَعِ كُواْ تَكُواْبِے؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai suka ce, “Allahn Ibraniyawa ya gamu da mu, muna roƙonka, ka bar mu mu yi tafiyar kwana uku cikin jeji domin mu yi wa Ubangiji Allahnmu hadaya, don kada ya aukar mana da annoba ko takobi.”