Exodus 5:8 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ku kuma bukace su su yi tubula daidai yawan tubalin da suka saba yi, kada ku rage. Ragwaye ne, shi ya sa suke kuka cewa, ‘Bari mu tafi mu yi hadaya ga Allahnmu.’
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكْدَهَكَ، كُبُڧَثٜىٰسُ سُيِيَوَنْ بُلُواكْ دَيْدَيْ يَدَّ سُكَيِ دَ ڢَرْكُواْ، كَدَ كُضَغٜىٰ مُسُ كُواْ غُدَا؞ أَيْ یَنْ ڧِوِيَنٜىٰ سُو! شِے يَسَا سُكٜىٰيِنْ كُوكَا سُنَ ثٜىٰوَ ‹عَبَرْمُ مُتَڢِے مُمِيڧَوَ اللَّهْ نْمُ هَدَايَ أَدَاجِ؞›
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk da haka, kada su kāsa cika yawan tubalin da aka ƙayyade musu da fari. Ai, su ragwaye ne, shi ya sa suke kuka, suna cewa, ‘A bar mu, mu tafi mu miƙa wa Allahnmu hadaya.’