Exodus 8:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka yi haka, da Haruna ya miƙa hannunsa da sandan, ya bugi ƙurar ƙasa, sai ƙwari masu cizo suka fito a kan mutane da dabbobi. Dukan ƙurar, ko’ina a ƙasar Masar ta zama cinnaku.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُوسَٰى دَ هَٰرُونَ كُوَ سُكَيِ حَكَ؞ هَٰرُونَ يَا مِيڧَ حَنُّنْسَ يَا بُغِ ڧُورَرْ ڧَسَا دَ سَنْدَنْسَ، سَيْغَا ݣُورْݣُوتَ سُكَذُواْ بِسَ مُتَنٜىٰ دَ دَبُّواْبِے؞ دُكَنْ ڧُورَرْ ڧَسَا تَذَمَ ݣُورْݣُوتَ عَكُواْعِنَ ثِكِنْ ڧَسَرْ مَصَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haka kuwa suka yi. Haruna ya miƙa sandansa ya bugi ƙurar ƙasa, sai ta zama kwarkwata a bisa 'yan adam, da bisa dabbobi. Dukan ƙurar ta zama kwarkwata ko'ina cikin ƙasar Masar.