Exodus 8:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da bokayen Fir’auna suka yi ƙoƙari yin sihiri iri na rufe ido domin su fito da kwari, sai suka kāsa. Ƙwari masu cizo kuwa suka rufe mutane da dabbobi.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مَاسُ دَبُواْ نَ ڢِرْعَوْنَ سُكَيِ ڧُواْڧَرِنْ يِنْ ݣُورْݣُوتَ تَهَنْيَرْسُ تَأَسِيرِ، عَمَّا بَسُ عِيَبَ؞ ݣُورْݣُوتَ سُكَ رُڢٜىٰ مُتَنٜىٰ دَ دَبُّواْبِے دُكَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Masu sihiri suka ƙokarta su sa kwarkwata ta bayyana ta wurin sihirinsu, amma ba su iya ba. Kwarkwata kuma ta yayyaɓe 'yan adam da dabbobi.