Exodus 8:21 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
In ba ka bar mutanena suka tafi ba, zan turo da tarin ƙuda a kanka da bayinka, a kan mutanenka da cikin gidajenka. Gidajen Masarawa za su cika da ƙudaje, har ma da ƙasa inda za su taka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عِدَنْ ڢَا كَڧِ كَبَرْ جَمَعَتَ سُتَڢِے، ذَنْعَيْكَ دَ تُلِنْ ڧُدَ عَكَنْكَ دَ دَتَّاوَنْكَ دَ مُتَنٜىٰنْكَ؞ غِدَاجٜىٰنْ مَصَرَاوَا ذَاسُ ثِثِّكَ دَ ڧُدَ، حَرْ مَا دَ ڧَسَا عِنْدَ سُكٜىٰ تَاكَاوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
In kuwa ka ƙi sakin jama'ata, sai in koro maka ƙudaje, da kai da fādawanka, da jama'arka, da gidajen Masarawa, har ma duk da ƙasa inda suke takawa.