Exodus 8:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Nilu zai cika da kwaɗi. Za su haura zuwa cikin fadanka da kan gadonka, cikin gidajen bayinka da kan mutanenka, cikin kwanonin toye-toyenka da na cin abincinka.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كُواْغِنْ نِلُ ذَيْثِكَ دَ ݣُوطِ، حَرْ سُڢِتُواْ سُشِغَ كُواْعِنَ ثِكِنْ غِدَنْكَ نَسَرْكِے دَ طَاكِنْ ݣُونْثِيَرْكَ حَرْ كَنْ غَدُوانْكَ دَ غِدَاجٜىٰنْ دَتَّاوَنْكَ دَ نَمُتَنٜىٰنْكَ؞ ذَاسُ كُمَ شِغَ وُرَارٜىٰنْ تُيَ غُرَاسَ دَ ݣُونُواْنِنْ ثِنْ عَبِنْثِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Nilu zai cika da kwaɗi, za su tashi, su shiga cikin fādarka, da ɗakin kwanciyarka, da gadonka, har da gidajen fadawanka da jama'arka. Za su kuma shiga matuyanka da kwanon tuwonka,