Exodus 8:5 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka ce wa Haruna, ‘Ka miƙa hannunka da sandanka bisa koguna da rafuffuka da kuma kududdufai, ka sa kwaɗi su fito su mamaye ƙasar Masar.’ ”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ وَ مُوسَٰى «ڢَطَا وَ هَٰرُونَ يَمِيڧَ سَنْدَنْ كِيوُانْسَ بِسَ دُكَنْ رَاڢُڢُّكَ دَ هَنْيُواْيِنْ ضُوَ دَ تَڢْكُنَ دُواْمِنْ أَسَا ݣُوطِ سُڢِتُواْ سُرُڢٜىٰ ڢُسْكَرْ ڧَسَرْ مَصَرْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Ubangiji ya ce wa Musa ya faɗa wa Haruna ya miƙa sandansa a bisa koguna, da rufuffuka, da tafkuna don ya sa kwaɗi su fito, su rufe ƙasar Masar.