Exodus 9:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ko’ina a Masar ƙanƙara ta bugi duk abin da yake a gonaki, mutane da dabbobi, ta bugi duk ganyaye da suke a gonaki, ta kuma ragargaza kowane itace.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڧَنْڧَرَرْ تَهَلَّكَرْ دَ كُواْوَنٜىٰ أَبِنْدَ يَكٜىٰ أَوَجٜىٰ كُواْعِنَ عَڧَسَرْ مَصَرْ، مُتَنٜىٰ دَ دَبُّواْبِے، تَلَلَتَرْ دَ ڟِرٜىٰ ڟِرٜىٰ نَڢِيلَيٜىٰ، حَرْ تَكَكَّرْيَ دُكَنْ عِتَتُوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ƙanƙarar ta bugi ko'ina a Masar. Dukan abin da yake cikin saura, mutum duk da dabba, da tsire-tsire duka, ƙanƙara ta buge su. Duk itatuwan da yake a saura aka ragargaza su.