Ezekiel 1:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kamannin halittun ya yi kamar garwashi mai cin wuta ko kuwa kamar fitilu. Wuta tana kai da kawowa a cikin halittun; ta yi haske ƙwarai, walƙiya kuma tana wulgawa daga cikinta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
غَا يَدَّ كَمَنِّنْ حَلِتُّو مَاسُ رَيْ يَكٜىٰ؞ عَڟَكِيَرْ حَلِتُّنْ، أَݣَويْ وَنِ أَبُ مَيْ كَمَ دَ غَرْوَشِنْ وُتَا مَيْثِ، كُواْ كَمَ دَ حَصْكٜىٰنْ ڢِتِلَ؞ أَبِنَّنْ يَنَ تَكَيْ دَ كَٰوُاْوَ أَڟَكَانِنْ حَلِتُّنْ؞ وُتَرْ كُوَ تَنَ حَصْكَكَاوَا، كُمَ دَغَ ثِكِنْ وُتَرْ، وَلْڧِيَ تَنَ ڢِتُواْوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A tsakiyar talikan akwai wani abu mai kama da garwashin wuta, kamar jiniyoyi kuma suna kai da kawowa a tsakanin talikan, wutar kuwa tana haskakawa. Daga cikin wutar kuma, sai ga walƙiya tana fitowa.